Rikicin neman shugabancin Jam’iyya ya kama jam’iyyar adawa ta PDP alhali wasu naso a bawa Arewa shugabancin Jam’iyyar.
Idan za’a iya tunawa, Adam Mu’azu shine tsohon Ciyaman din Jam’iyyar kafin yayi murabus bayan da aka kada su zabe a watan Maris 2015.
Mataimakin shi Uche Secondus wanda dan Rivers shi shi ya zama mukaddashin Ciyaman din Jam’iyyar. Wani rahoto daga jaridar The Punch ya nuna cewa Ahmed Gulak yaje hedikwatar jam’iyyar inda ya nemi Secondus da yayi murabus.
Inda yake zantawa da yan jarida, Gulak yace: “Naje ne domin in bayyana niyya ta ta maye gurbin tsohon Ciyaman din Jam’iyya wanda yayi murabus.
“Ni a matsayina na dan Jam’iyya na san akwai gibi, kuma kundun tsarin mulki na Jam’iyya ya bada dama. Tsohon Ciyaman yayi murabus ne kila saboda faduwar da Jam’iyya tayi. PDP na bukatar shugabanci na gari a yanzu. Abunda tsarin mulki yace shine, idan wani yayi murabus, wani daga yankin daya fito ya gaje shi.”
Gulak kuma yayi kira ga gwamnan jihar Ekiti daya kama bakin shi domin shi bai san yadda ake gudanar da Jam’iyyar dayake a ciki ta PDP.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Rikicin Neman Shugabancin Jam’iyya Ya Kama PDP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Rikicin Neman Shugabancin Jam’iyya Ya Kama PDP
No comments:
Post a Comment