Wednesday, 30 September 2015

Sojojin Najeriya Sun Kashe Wani Babban Dan Boko Haram

Sojojin Najeriya sun kashe wani babban dan boko Haram a lokacin da suka kai hari a Kwatarha da Torikwaptar a karamar hukumar Gwoza.



Sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya



A cewa Mukaddashin Daraktan labarai na Sojin Kasa, Kanar Sani Usman, dan ta’addan ya dade yana jawo barna babba a wadannan garuruwan. Jaridar Punch ta ruwaito.


Yace: ”An kashe shi ne a lokacin da sukayi artabu da sojin Najeriya a ranar Litinin da Yamma.”


Kanar Usman ya bayyana cewa Yan Boko Haram hudu sun ruga amma anji masu raunuka. Sannan an samu bindigar AK 47 daga hannun su.


Mukaddashin Daraktan kuma ya bayyana cewa Sojojin Dibishan ta 3 na Soji sun kama wani babban Dan Boko Haram a Yobe.


Wanda aka kama sunan shi Alhaji Tijjani Usman Damagun a garin Damagun.


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.



The post Sojojin Najeriya Sun Kashe Wani Babban Dan Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



Sojojin Najeriya Sun Kashe Wani Babban Dan Boko Haram

No comments:

Post a Comment