Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Babatunde Raji Fashola yayi Allah wadai da yan boko Haram. Jaridar Punch ta ruwaito cewa Fashola ya fadi haka ne a lokacin da ake gabatar da wani littafi mai suna: “Frontiers of Jihad: Radical Islam In Africa,” wanda Dacta Yinka Olomojobi ta rubuta. Yan gabatar dashi a MUSON, Onikan a Jihar Legas.
Yan Boko Haram da Shugaban su Abubakar Shekau
Gwamnan ya bayyana cewa yan Boko Haram suna hure ma mutane kunnuwa amma su kansu basu tsare dokokin Musulunci.
“Mun bari wasu yan kadan sun bata suna amfani da sunan wani addini suna batan sunan wasu Biliyoyin mutane a fadin duniya masu son zaman lafi. Su kansu suna karya dokokin addinin da suke ikirarin suna bi.”
Fashola yayi godiya ga ma marabucin akan irin gudunmuwar daya bada a cikin littafin nashi.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Yan Boko Haram Ba Musulmai Bane – Fashola appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Yan Boko Haram Ba Musulmai Bane – Fashola
No comments:
Post a Comment