Wednesday, 2 September 2015

Kwana 100: Wani Jigon Dan PDP Ya Yaba Ma Buhari

Shugaban Kasa Buhari ya samu yabo daga wani jigon dan PDP, Abubakar Dogonyaro Bibi.



A rahotan Jaridar  The Sun, Abubakar Bibi ya bayyana cewa kwanaki 100 na Buhari masu nuni ne da alkairi. Sannan kuma ya musanta masu cewa Buhari baya sauri.


Yace: “Idan muka lura za muga kullum manyan Sakatarori na kowace ma’aikata suna zuwa suna bashi bayanin yadda suke gudana da ma’aikatun.


“Buhari ba zaya nada Ministoci ba har sai yasan mi akeyi a kowace ma’aikata, shige da ficenta. Idan za’ayi gaskiya, Shugaba Buhari na kokartawa musamman wajen sha’anin tsaro. A mtsayin shi na shugaban kasa yayi kokari sosai.”


Da aka tambaye shi ko yana gani Buhari yana waje wasu yan bangare a Najeriya sai Bibi yace: “Toh wannan sai dai mu tsaya mu gani nan da wata 2 ko 3 a lokacin da ya nada Ministocin shi.”


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.



The post Kwana 100: Wani Jigon Dan PDP Ya Yaba Ma Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



Kwana 100: Wani Jigon Dan PDP Ya Yaba Ma Buhari

No comments:

Post a Comment