A lokacin da Najeriya ke bikin cike shekaru 55, mutum daya da yan Najeriya ke tunawa shine Taiwo Akinkunmi wanda ya zana tutar Najeria. Kuma ya buri akan Najeriya.
Taiwo Akinkunmi wanda ya zana tutar Najeria
A shekara 25, Taiwo yana Kwalajin Fasaha dage a kasar Norwar. A inda ya zana tutar a 1958.
Watannin kadan da suka wuce ana jita jita cewa Taiwo ya mutu. Wannan ya sanya Naij.com tayi tattataki zuwa inda yake. Dan haka zamu iya cewa kai tsaye, Taiwo yana nan a raye.
Gidan shi na nan Ibadan inda aka yi ma gidan Fenti da kalar tutar Najeriya na Tsanwa da Fari da Tsanwa.
Lokacin da wakilin mu ya fara zuwa sai ya hadu da babban, dan shi Akinwumi Akinkunmi wanda ya bayyana cewa, baban shi na nan da rai, amma dai baya da lafiya.
Wakilin Naij.com ya samu haduwa da Taiwo Akinkunmi inda suka gaisa sosai. Ya bayyana cewa yazo ya tattauna akan yadda akayi ya zana tutar amma rashin lafiya baza ta bar shi ba. Sai yace:
“Ina yin murnar zagayowar ranar Yancin Kan Najeriya. Ina fatan Najeriya zata zama babbar kasa, kuma ta cigaba da cigaba da samun zaman lafiya.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Nigeria At 55: Buri Akan Najeriya – Taiwo Akinwumi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Nigeria At 55: Buri Akan Najeriya – Taiwo Akinwumi
No comments:
Post a Comment