Janar Buratai, Hafsin Sojin kasa ya jagoranci sojojin a ranar Juma’a, 2 ga watan Oktoba wajen Paretin safi.
Janar Tukur Buratai Shugaban sojojin kasa
Wannan ba shine karo na farko da shugaban Sojojin na nuna damuwar ga Sojojin shi ba domin ya tabaa kwana a Gambaru inda yan Boko Haram suka dade suna rike dashi.
Janar Buratai shine Hafsin soja na farko wanda ke yin haka domin mafi yawanci sunfi so su zauna gida su bada umurni.
A lokacin zuwan nashi, Hafsin ya gargadi sojojin shi inda yake ce masu akwai sauran aiki a gaban su.
Buratai kuma ya kara jadda cewa lallai zasu kawo karshen Boko Haram kamar yadda shugaban Kasa ya umurce su.
The post Janar Buratai Ya Jagoranci Sojoji Wajen Paretin Safe appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Janar Buratai Ya Jagoranci Sojoji Wajen Paretin Safe
No comments:
Post a Comment