Friday, 31 July 2015

Shugaban Yan Sanda Ya Ba Matukan Motoci Wa’adin Sati Biyu Kawai

 Solomon Arase, Shugaban Yan Sandan Najeriya yaba matukan motoci na Abuja sati 2 suyi rajistar motocinsu.


Arase yace wannan ne a lokacin da shuwagabannin kungiyar ta Kasa da Jihohi ta Masu sana’ar tukin mota NURTW’ a Abuja


Yace: ‘’Shugaba da Sakateran Zan ba ku alfarmar sati biyu wanda daga bisani zamu faru kama duk wani abun hawa da baya da rijista kuma suke yawo akan babban birnin na Abuja (FCT).’’


Yace kamen zaya fara daga FCT ne saboda shi babban birni ne. Saboda kuma wasu na yawo basu biyan haraji.


Yace Lambar motoci ba launi yafi motoci da launi. Yace: ‘’Akwai tazi da yawa mararsa fenti a Abuja. Zamu magance abun tun kafin ya zama matsala. Akwai yan kabu kabu da yawa a Abuja masu yawo babu rajista.”


Yaba Shugabannin Jihohin na Kungiyar NURTW shawara akan su tabattar yan kungiyar tasu tayi rajista da inshora domin motincinsu.


Arase yace, a ko yaushe yan sanda muna samun matsaloli da matukan motoci a manyan hanyoyi domin rashin rajista. Wancan shine abunda muke so kungiyar nan taku ta NURTW ta wayar ma ya’yanta da kai.


Ya roki yan kungiyar NURTW da su bawa yan sanda bayyani mai amfani akan yadda su ringa yin aikin su ga al’umma yadda ya kamata.


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.


The post Shugaban Yan Sanda Ya Ba Matukan Motoci Wa’adin Sati Biyu Kawai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



Shugaban Yan Sanda Ya Ba Matukan Motoci Wa’adin Sati Biyu Kawai

No comments:

Post a Comment