Labarai sun nuna cewa tsohon shugaban kasa Obasanjo ne ya sanya Buhari ya canza ra’ayin shi kuma ya sanya baki cikin rikicin majalisa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wayar da Obasanjo ya buga ma Buhari ya sanya shi ya canza ra’ayin shi kuma ya sanya baki a ciki. Wanda hakan ne ya Kawo karshen rikici kuma Femi Gbajabiamila ya samu kujerar shugaban majalisa.
Bayan da Yakubu Dogara ya zama kakakin majalisa, Shugaba Buhari ya kauracema sanya baki cikin rikicin daya tashi.
Wasu shuwagabannin jam’iyyar ta APC a majalisar a karkashin wata kungiya mai suna “masu kishi” sunyi niyar suje wajen Buhari ko kuma na kusa da shi domin su sanya shi ya sanya baki cikin rikicin. Daga baya sai sukaje wajen Obasanjo domin sun san Buhari na girmama shi domin yayi mashi magana. Bayan da suka gama bayani, Obasanjo sai ya kira Buhari yayi mashi bayanin matsalar da rikicin zai iya kawowa idan ba’a magance shi yanzu ba. Yace mashi “Idan dai sanya bakin naka zaya Kawokarshen rikicin kuma ya kawk cigaban Damakaradiyya a Najeriya ya kamata ka sanya.”
Wata majiya tace: “Munyi imani cewa hakan ne ya sanya shi ya sanya baki a cikin rikicin”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Obasanjo Ne Ya Matsa Na Buhari Ya Sanya Baki A Cikin Rikicin Majalisa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Obasanjo Ne Ya Matsa Na Buhari Ya Sanya Baki A Cikin Rikicin Majalisa
No comments:
Post a Comment