Thursday, 30 July 2015

Ba Zany Aiki Da Gwamnatin Buhari Ba – Tsohon Ma’aikacin Buhari

Yinka Odumakin, tsohon mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari lokacin zaben shugaban kasa a 2011 yace ba za yayi aiki a karkashin Shugaba Buhari koda shi ya nadanshi


Mista Odumakin wanda shine Sakateran Mai magana da yawun kungiyar Yarabawa ta kasa ‘’Afenifere.’’ Ya fadi hakan lokacin firar sa da yayi da Jaridar Vanguard.


‘’Ban goyi bayan kungiyar APC ba a lokacin yakin neman zabe. Ni ba cima kwance bane. Akwai ire iren mu, wadanda suna iya bambance tsakanin abun da keda kyau da abu marar kyau. Ba zanyi hakan ba don wani dalili.’’  Yace wannan magana ne inda suka tambaye shi ko zai karbi wani mukami a gwamnatin Buhari.


Kuma yace: ”Baiyi nadama ba don ya goyi bayan tsohon shugaba Goodluck Jonathan a zaben shugaban kasa daya wuce. Ya shawarci mutanen Najeriya akan cewa suba Shugaba Buhari lokaci, cewa kada mhtane suyi saurin Yanke hukunci akan gwamnatin ta Buharin.


”Inna tunanin bai da kyau inyi tsokaci akan gwamnati da bata wuce kwanar 40 akan mulki.”


Ku karanta hirar gaba daya acikin Jaridar Vanguard.


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.


The post Ba Zany Aiki Da Gwamnatin Buhari Ba – Tsohon Ma’aikacin Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



Ba Zany Aiki Da Gwamnatin Buhari Ba – Tsohon Ma’aikacin Buhari

No comments:

Post a Comment