Jam’iyyar APC ta jihar Ekiti ta nunaa rashin jin dadin ta akan yadda ake yin ammafani da gidan Rediyo da Talabijin ana batanci ga jam’iyyun adawa.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, jam’iyyar APC ta jihar ta bayyana hakan ne a wata wasika data rubuta wa Kwamishan din watsa labarai ta kasa (NBC) a akan abubuwan da sukeyi wadanda basu dace ba a ranar 24 ga watan Yuli.
Dama dai NBC ta caji kafacen watsa labaran Naira 500,000, amma ita jam’iyyar tace har yanzu basu bar yin abunda bail dace ba.
Mai magana da yawun jam’iyyar jihar ta APC, Taiwo Olubusun yace: “Har yanzu dai ba’a bar yin amfani da kafafen watsa labarai wajen farma yan adawa ba. Abun takaici dai har yanzu basu canza ba. Har yanzu sauna sanar da mutane karai raki akan yan adawa.”
Shugaban gida Talabijin Na jihar Lere Olayinka ya musanta zancen cewa suna yin abunda bai kamata ba a wani shiri da sukeyi da Yarbanci mai sauna “Lari Inu Aka.”
“Biodun Ilori da Kayode Felegan sun karanta wani labari na karya wanda suka ce wata jaridar kasa ta rubuta game da yanayin aikin su da kuma akan Lere Olayinka. Wannan zancen karya ne saboda babu jaridar data hi hakan. Kuma sunyi karya akaina ni Taiwo Olubunso, wai wani babban kunburi kafa ta keyi saboda ina kalubalantar gwamna Ayodele Fayose. Suka ce wai wani mai bada maganin gargajiya ga shawarci ni inje in bashi gwamnan hakuri. Hakan da sukayi ya matukar kunyata ni , iyali na da abokai na. Kuma hakan ya taba lafiya ta. Sunce wai naje a asirci ina rokon gwamna Ayodele Fayose gafara amma ina fitowa cikin mutane ina zagin shi.” Yace.
Bisani dai ita jam’iyyar ta PDP ta rabo gida biyu a Ekitin. Bangare daya na biyayya ga gwamna Fayose, daya Kuma sun kori mutanen shi daga shugabancin jam’iyyar.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Jam’iyyar APC Tayi Allah Wadai Da Batancin Da Ake Yi Mata A Kafafen Watsa Labarai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Jam’iyyar APC Tayi Allah Wadai Da Batancin Da Ake Yi Mata A Kafafen Watsa Labarai
No comments:
Post a Comment