Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Juma’a 28 ga watan Agusta. Ku duba domin ku same su.
1. Shin gwamnatin Buhari ta Yan Arewa ce?
Wasu Yan Najeriya na zargin shugaba Buhari ta nada Yan Arewa kawai a cikin gwamanatin shi.
2. Manyan Jam’iyyar APC sun zargi Buhari da nada Yan Arewa kawai.
Wasu manyan Jam’iyyar APC sun zargi shugaba Buhari da nada Yan Arewa kawai a cikin gwamnatin shi. Wannan na zuwa ne bayan nade naden da yayi a wannan satin.
3. Wasu abubuwa akan sabon shugaban Kastam
Bayanai nata kara bayyana akan sabon shugaban Kasatam da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada, Kanar Hamidu Ali.
4. Wa ya gayyaci Al Assiri zuwa Najeriya.
Bayanai nata kara fitowa akan cewa wannann dan ta’addan na kasar Labanon, Ahmed Al Assir yayi yunkurin zuwa Najeriya ne saboda wani Kamfani daya gayyace shi.
5. Babbabn Soja yayi wani bayani akan yan Boko Haram.
Mukaddashin Daraktan labarai na Sojin Kasa, Kanar Sani Kakasheka Usman ya bayyana cewa wasu yan Boko Haram ku Al Kur’ani basu iya karanatawa.
6. Ka bincike kowa da kowa – Cif Mbazulika Ameachi.
Tsohon mMinistan sufurin Jiragen Sama a Jamhuriyya ta 1 ya shawarci shugaba Buhari ya nuna ma duniya cewa da gaske yake wajen yaki da rashawa ta hanyar bincikar yan Jam’iyyar shi.
7. An gano Jami’o’i 57 na bogi.
An gano cewa akwai kimanin makarantu 57 na bogi wadanda ke bada takardar Digiri na karya a Najeriya. Hukumar Jami’o’in Najeriya (NUC) ce ta bayyana hakan.
8. An nada diyar AtikuKwamishina, ta saudar da albashinta, alawunsu dinta.
Diyar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, Dacta FAtima Atiku ta bayyana cewa ta sadaukar da albashint domin gyara asibitocin Jihar Adamawa. Ta bayyana hakan ne bayan da aka bata Kwamishinan lafiya.
9. Dalilin daya sanya naje wajen Buhari, Tinubu – shugaban Majalisar Dattawa.
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa zuwan da yayi wajen shugaba Buhari da kuma shugaban Jam’iyyar APC, Tinubu, ba shida wata alaka da rikicin da akeyi a cikin majalisar.
10. Sabon nadin da Sifeton Yan Sanda yayi.
Sifeto Janar na Yan Sanda Solomon E Arase ya nada ACP Olabisi Alofe Kolawole a matsayin sabon Jami’i mai hudda da Jama’a na ‘yan sanda.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Manyan Labarai Guda 10 Da Sukayi Fice A Ranar Juma’a 28 Ga Watan Agusta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Manyan Labarai Guda 10 Da Sukayi Fice A Ranar Juma’a 28 Ga Watan Agusta
No comments:
Post a Comment