Majalisar matasa ta Igbo (OYC) ta bayyana tsananin rashin gamsuwar ta akan yadda shugaba Buhari yayi nade nade a wannan makon.
A wannan satin ne shugaba Buhari ya nada Babachir David Lawai a matsayin sakataren gwamnatin Tarayya, sannan kuma ya nada Abba Kyari a matsayin shugaban ma’aikatan shi.
A wani rahoto daga Jaridar Vanguard ya bayyana cewa shugaban kungiyar Mazi Okechukwu Isiguzoro ne ya sanya mata takardar manema labaran hannu tare da Jami’i mai hudda da Jama’a, Obinna Adibe a ranar Juma’a 27 ga watan Agusta.
Isiguzoro ya jadda cewa cewa nade naden da Shugaba Buhari yayi abin Allah wadai ne kuma ya saba da tsarin kasa (Federal Character) kamar yadda ya tabbata a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Yace nade naden ya tabbatar da tsanar da Shugaba Buhari yayi ma Igbo duk da cewar shi shugaba Buhari ” shi ba na kowa bane, shi na kowa ne.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Nade Naden Da Buhari Yayi Ya Nuna Yana Kin Jinin Igbo -Ndigbo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Nade Naden Da Buhari Yayi Ya Nuna Yana Kin Jinin Igbo -Ndigbo
No comments:
Post a Comment