A ranar Juma’a 27 ga watan Agusta, Majalisar Dattawa ta sha alashin taimaka ma masu saka hannun Jari da dokokin da zasu tallafa ma kasuwanci a Najeriya.
Wannan na zuwa ne a lokacin da Muhmmadu Sanusi II, Ciyaman din Kamfanin Balck Rhino ya jagoranci Stephen Schwarzman, Ciyaman din Kamfanin Black Stone zuwa gaisuwar bangirma ga shugaban Majalisar Dattawa.
A cikin tawagar hadda Alhaji Aliko Dongote.
Shugaban Majalisar ya bayyana cewa, Majalisa ta 7 ta sake duba dokokin laifufka na Najeriya. Mu kuma zamu duba na kasuwanci a wannan Majalisar.
Saraki yace: “Ina mai tabbatar maka da cewa wannan majalisar za tayi duk abunda ya kamata wajen yin dokoki wadanda zau taimaka ma kasuwanci da zuba hannun Jari a Najeriya.”
Shi kuma Muhammadu Sanusi II sai yace: “Nazo nan a matsayina na Ciyaman din Kamfanin Black Rhino. Muke yin aiyukan na gine ine domin cigaban Afiriki. Mun shirya wani hadin gwiwa da Kamfanin Dangote domin mu samar da wuta da kuma hanyoyin.”
Mista Schwarzman yayi ma Shugaban Majalisar Dattawan murnar nasaran daya samu aka zabe shi shugaban Majalisar Dattawa.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Tallafa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Tallafa
No comments:
Post a Comment