Monday, 31 August 2015

Saraki Zaya Jagoranci Tawagar Najeriya Zuwa Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Majalisar Dattawa Dacta Abubakar Bukola Saraki zaya jagoranci tawagar Najeriya zuwa Majalisar Dinkin Duniya domin gudanar da taron Yan Majalisa na duniya.



A wanna taron, ana sa ran Sakataren Majalisar Dinmin Duniya zaya bude taron inda za’a gabatar da rahotanni da kuma tattaunawa akan “Damakaradiyya a lumana domin cigaba.”


Wasu abubu da za’a tatauna sun hada da; Matsalolin da majalisu ke fuskanta, yadda zasu ringa duba aiyukan masu gabatar wa. Idan gama wannan, Shugaban majalisar kasar Isira’ila  Yuli-Yoel Edelstein zaya gana da Saraki.


Saraki zaya gabatar da jawabin shi a ranar Laraba 3 ga watan Agusta. Cikin yan tawagar shi sun hada da Sanata Andy Uba, Shehu Sani da Dino Melaye.


Sannan kuma akwai Mai tamaka mashi akan harkokin tattalin arziki  Dacta Uchendu Okoye da kuma maitaimaka mashi akan hadin gwiwa.


Tawagar Shugaban Majalisar ta tafi Amurka inda za’a gabatar da taron a ranar Asabar 29 ga watan Agusta ta filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.



The post Saraki Zaya Jagoranci Tawagar Najeriya Zuwa Majalisar Dinkin Duniya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



Saraki Zaya Jagoranci Tawagar Najeriya Zuwa Majalisar Dinkin Duniya

No comments:

Post a Comment