Wednesday, 26 August 2015

Manyan Kudu Sun Soki Buhari Da Kabilanci

A ranar Laraba 25 ga watan Agusta, Shuwagabannin Kudu sun zargin shugaba Buhari da kabilanci wajen nade naden mukamin da yayi.



Kungiyar mai suna Kungiyar mutanen kudancin Najeriya ”Southern Nigeria Peoples Assembly (SNP)” a wani taro da aka gudanar a Akure, jihar Ondo.


Kungiyar SNP wadda ke samun jagoranci daga  Cif Edwin Clerk, tsohon kwamishinan labarai na gwamnatin tarayya ya nuna goyan bayan ta akan yaki da rashawa, amma ta nuna rashin gamsuwar ta akan yadda shugaba Buhari yake nade nade.


Edwin Clerk dai yana tare da Sanata Femi Okurounmo, Ciyaman din rantsar da taron kasa na 2014, Rev Emmanuel Gbongi, shugaban mutan kudu maso yamma, da Alex Ekweme, tsohon Mataimakin shugaban kasa.


Sauran kuma sun hada da Minista na Jamhuriyya ta 3, Ngoji Denton-West, tsohon Minstan Sufuri, Cif Ebenezer Babatope, Farfesa Ikechukwu Madubuike, Kola Olajide, Ndongesit Ekang.


Sanna kuma akwai Sanata Tony Adefuye, tsohon gwamnan jihar Legas, Sanata Kofoworola Bucknor-Akerele, da Farfesa Olu Agbi.


Clerk yace: “Kokarin da Shugaba Buhari yakeyi domin yakar rashawa abunyin maraba ne. Hakan zaya bada dama masu zuba hannun jari suzo su sanya domin cigaban Najeria.


“Amma wani abu a nan shine, bai kamata a iyakance binciken a akan abokan adawa ba kawai. Domin yin hakan ba zaya haifar da Da mai ido ba.


“Mu a matsayin mu na yan Najeriya duk guda ne. Muna so muyi kira ga shugaban kasa ya duba yan Najeriya ba wai wadanda suka bashi kuriya ba. Yace ‘ shi na kowa ne, kuma shi ba na kowa bane.”


Gbonigi shima yayi kira ga shugaban kasa da kada ya bincike wasu ya kyale wasu. Yace mutane koda na kusa dashi ne to ayi abunda ya kamata.


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.



The post Manyan Kudu Sun Soki Buhari Da Kabilanci appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



Manyan Kudu Sun Soki Buhari Da Kabilanci

No comments:

Post a Comment